Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiChina ta soki zargin Amurka na ta’azzara rashin tsaro a Najeriya

China ta soki zargin Amurka na ta’azzara rashin tsaro a Najeriya

Ƙasar China ta yi watsi da zargin da wasu mambobin majalisar dokokin Amurka suka yi cewa ƙasar na tallafa wa ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a Najeriya tare da biyan wasu ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai domin kare muradun kasuwancinsu.

Ofishin jakadancin China a Abuja ya bayyana zargin a matsayin wanda bai da tushe, kuma yana cutar da dangantaka tsakanin China da Najeriya.

Zargin ya samo asali ne daga wani ƙudirin neman a dauki mataki kan Najeriya bisa zargin musguna wa Kiristoci, wanda ya hada da batun cewa masu aikin haƙar ma’adinai na China a Najeriya na biyan kuɗaɗe ga wasu ƙungiyoyin masu dauke da makamai.

Rahotanni daga shekarar 2023 sun nuna cewa wasu ‘yan ƙasar China da ke haƙar ma’adinai a wurare kamar Zamfara na iya kasancewa sun taimaka kai tsaye ko a kaikaice wajen tallafa wa ƙungiyoyin masu dauke da makamai da ke neman mallakar wuraren hakar ma’adinai masu riba.

Ofishin jakadancin dai ya jaddada cewa yawancin kamfanonin hakar ma’adinai na China a Najeriya suna bin dokokin ƙasa, suna bayar da gudummawa ga al’umma ta hanyar samar da ayyukan yi da tallafa wa ci gaban cikin gida.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments