Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKano: Shaguna 85 sun kone kurmus a kasuwar yan katako

Kano: Shaguna 85 sun kone kurmus a kasuwar yan katako

Kusan shaguna 85 ne suka kone kurmus sakamakon gobara a kasuwar yan katako dake rijiyar lemo

Aƙalla shaguna 85 ne suka ƙone ƙurmus sakamakon gobarar da ta tashi a wasu sassan kasuwar ƴan Katako da ke Rijiyar Lemo, a Ƙaramar Hukumar Ungogo ta jihar Kano, a safiyar Laraba.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:28 na Asuba, bayan da ta samu kiran gaggawa daga Kabiru Nafi’u wanda ya sanar da tashin gobara a kasuwar.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar, ya ce:

“Da isar jami’anmu, sun tarar da kasuwar katako mai girman kafa 500 da 500 tana ci da wuta.

“Kimanin manyan shaguna 30 da kuma ƙananu 55 sun ƙone gaba ɗaya.”

Ya ce sun tura jami’an kashe gobara daga tashoshin Dawanau, Rijiyar Zaki da Bompai nan take, inda aka yi amfani da motocin kashe gobara uku domin shawo kan gobarar.

Ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar.

SourcePremier
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments