Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon Shugaban hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON).
Mashawarcin Shugaban kasa a kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwar a ranar Laraba.
Ya ce:
“Shugaba Tinubu ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wasiƙa yana neman a gaggauta tantancewa da amincewa da naɗin Ambasada Yusuf domin maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman, wanda ya yi murabus a wannan mako bayan kusan watanni 14 a kan muƙaminsa.”
Naɗin zai fara aiki ne bayan Majalisar Dattawa ta amince da shi, bisa tanadin Sashe na 3(2) na Dokar NAHCON.
Ambasada Yusuf ƙwararren jami’in diflomasiyya ne. Ya taba zama Jakadan Najeriya a ƙasar Türkiye daga 2021 zuwa 2024.
Farfesa Abdullahi Usman ya yi murabus ne a ranar Litinin, bayan fiye da shekara guda da fara aiki. M
Murabus ɗin ya zo a wani muhimmin lokaci, yayin da shirye-shiryen aikin Hajjin 2026 suka fara kankama.