Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiFadar shugaban kasa na shirin daina amfani da wutar lantarki ta kasa...

Fadar shugaban kasa na shirin daina amfani da wutar lantarki ta kasa bayan samar da solar

Fadar shugaban kasa ta Aso Rock za ta katse amfani da wutar lantarki daga babban layin wutar na kasa, nan da watan Maris 2026, bayan kammala aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana (solar).

Babban sakataren fadar, Temitope Fashedemi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake kare kasafin kudin fadar gwamnati na shekarar 2026 a gaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkoki na musamman.

Cikin bayanan zaman da Fadar Shugaban Kasa ta aikewa wakilan kafafen yada labarai a yammacin ranar Laraba, ya shaida wa kwamitin, wanda Sanata Kaka Lawan mai wakiltar Borno ta Tsakiya ke jagoranta, cewa an kammala sanya na’urar samar da wutar ta hasken rana ne a karshen shekarar 2025, kuma tun daga watan Disamba ake gudanar da gwaje-gwaje domin tabbatar da ingancinta.

SourcePremier
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments