Rigimar siyasa a Jihar Rivers na iya lafawa bayan shiga tsakani da Shugaba Bola Tinubu ya yi.
A cewar jaridar The Nation a ranar Litinin, an ruwaito cewa Shugaban ya yi tattaunawa da Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike, Gwamnan Jihar Rivers Siminalayi Fubara, da sauran manyan shugabanni daga jihar.
Jaridar ta kara da cewa Gwamna Fubara ya raka Wike zuwa gidansa da ke Guzape, Abuja, bayan kammala tattaunawar.
Rahoton ya nu na cewa ana zargin Fubara ya roƙi ministan, yana mai alƙawarin cewa ba zai sake nuna masa rashin girmamawa ba, wanda hakan ke nuna yiwuwar sulhu tsakanin manyan ‘yan siyasa na jihar.