Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKwara: Tinubu ya gana da Gwamna AbdukRazaq a kan harin da ya...

Kwara: Tinubu ya gana da Gwamna AbdukRazaq a kan harin da ya kashe mutum sama da 100

Tinubu ya gana da gwamnan jihar Kwara, AbdulRazaq, dangane da harin da ya kashe sama da mutum 100.

Gwamnan Jihar Kwara kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin ƙasar nan, AbdulRahman AbdulRazaq, ya gana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, biyo bayan harin da aka kai garin Woro da ke karamar hukumar Kiama jiharsa.

Wannan na cikin sanarwar da Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan kan Kafafen sada zumunta, Akeweje Olayinka Fafoluyi, ya fitar a ranar Alhamis 5 ga Fabrairu 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya gode wa Shugaban Ƙasa bisa kafa rundunar tsaro nlta Operation Savannah Shield da kuma tura dakarun soji zuwa yankin, yana mai cewa matakin zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya da tsaro.

Ya ƙara da cewa kafin ganawar, Gwamna AbdulRazaq ya ziyarci Kaiama tare da manyan jami’an tsaro da wasu mambobin majalisar zartarwar jihar, domin duba halin da yankin ke ciki bayan harin.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments