Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnonin Arewa sun bayyana takaicinsu kan kisan gillar da aka yi a...

Gwamnonin Arewa sun bayyana takaicinsu kan kisan gillar da aka yi a Katsina, Kwara da Benue.

Gwamnonin yankin Arewa sun yi tir da hare-haren da suka yi sanadin asarar rayuka a Katsina, Kwara da Benue.

Ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta yi Alla-wadai da kashe-kashen mutane a jihohin Katsina, Kwara da kuma Benue, inda suka kwatanta hakan a matsayin rashin imani kuma cin mutunci ga ƙasa.

Hakan na zuwa ne bayan munanan hare-haren da aka kai karamar hukumar Kaiama na jihar Kwara, inda waɗanda ake kyautata zaton ƴan bindiga ne suka kutsa jihar ranar Talata tare da kashe sama da mutum 100.

Sai dai kuma harin karamar hukumar Faskari a jihar Katsina wanda ya hallaka aƙalla mutum 20, sai kuma wani hari na daban a karamar hukumar Kwande na jihar Benue da ya janyo mutuwar mutane da dama.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments