Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSaudiyya na shirin bai wa raƙuman ƙasarta fasfo

Saudiyya na shirin bai wa raƙuman ƙasarta fasfo

Ƙasar Saudiyya ta sanar da shirinta na fara bai wa miliyoyin raƙuman da ke ƙasar fasfo, domin inganta kula da su da kuma sauƙaƙa tsarin gudanar da muhimmin fannin kiwon raƙuma.

Wani saƙo da ma’aikatar muhalli, ruwa da noma ta wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna hoton fasfon, wanda ke da launin kore, tare da tambarin ƙasar da kuma hoton raƙumi mai launin zinariya.

A shekarar 2024, gwamnatin ne dai Saudiyya ta ƙiyasta cewa akwai kusan raƙuma miliyan biyu da dubu dari biyu a ƙasar.

Saudiyya kuma na shirya gasar kyau na raƙuma a lokacin bukukuwan shekara-shekara, lamarin da ke nuna muhimmancin raƙumi a al’adu da tattalin arziƙin ƙasar.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments