Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSojojin Najeriya sun kashe kwamandan Boko Haram na biyu a Sambisa

Sojojin Najeriya sun kashe kwamandan Boko Haram na biyu a Sambisa

Sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe wani babban Kwamandan Boko haram a sambisa

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe wani babban kwamanda a kungiyar Boko Haram da kuma wasu ‘yan kungiyar 10 a samamen da ta kai a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin kasar.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce Abu Khalid shi ne babban kwamandan Boko Haram na biyu a dajin Sambisa.

Ta ce ya taka rawa wajen kitsa hare hare da dama da mayakan kungiyar suka kai a yankin.

Najeriya dai ta jima tana fama da matsalar hare haren masu ikirarin jihadi inda har abin ya kai ga an samu wasu ‘yan bindiga da ke satar mutane don karbar kudin fansa a kasar.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments