Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wasu ma’aurata da aka bayyana da sunayen Fred da Goodness bisa zargin shirya satar kansu da kansu, tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 10 daga iyalansu da abokai.
Rahotanni sun nuna cewa ma’auratan sun ƙirƙiri labarin an sace su ne domin tara kuɗin da mijin ke bukata don komawa Amurka, sakamakon rashin tallafin kuɗi daga masu ɗaukar nauyinsa.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar 7 ga Janairu, 2026, lokacin da ma’auratan suka tuntubi ‘yan uwa daga bangarorin iyalai biyu, suna sanar da su cewa an yi garkuwa da su, tare da buƙatar a tura kuɗin fansa cikin gaggawa.
Saboda tsoro da damuwa, iyalan sun haɗa kai, suka tara N10m cikin kwanaki uku, suna zaton hakan ne kaɗai zai ceci rayukan ‘yan uwansu.
Wata majiya daga rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa shirin an yi shi ne da amincewar ma’auratan gaba ɗaya. Ta ce mijin yana da niyyar komawa Amurka, amma saboda rashin kuɗi, suka yanke shawarar shirya satar kansu a matsayin hanya ta tara kuɗi cikin sauri.
Wannan ya sa suka yaudari dangi da abokai, suna nuna cewa suna cikin hatsari. Yanzu haka dai jami'an tsaro an ci gaba da bincike kafin a gurfanar da su a gaban kotu.