Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaGanduje ya isa Abuja daga Landan don bikin karɓar Abba zuwa APC

Ganduje ya isa Abuja daga Landan don bikin karɓar Abba zuwa APC

Ganduje ya dawo Abuja daga London domin tarbar Abba Kabir Yusuf zuwa APC

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje, ya koma Najeriya daga Birtaniya a yau Litinin, yayin da jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ke shirin karɓar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bayan ficewarsa daga NNPP a makon da ya gabata.

A yau ne ake sa ran gwamna Abba Kabir zai sanar da komawa jam’iyyar APC a hukumance bayan raba gari da ubangidansa a siyasa, Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda shi ne jagoran jam’iyyar NNPP lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ke a tsakanin ɓangarorin siyasa a Kano, jiha mafi yawan al’umma a Arewacin Najeriya.

Wata sanarwa da Kwamared Muhammad Garba, shugaban ma’aikatan Abdullahi Ganduje, ya fitar, ta ce ana sa ran tsohon gwamnan “zai taka muhimmiyar rawa a bikin karɓar Gwamna Abba Kabir, wanda ake sa ran zai sauya sheƙa zuwa APC” a yau Litinin.

Ganduje ya tafi Birtaniya ne domin halaratar bikin kammala karatun digiri na biyu na ‘yarsa Fatima Ganduje a jami’ar King’s College, London. wadda ta kammala karatunta a ranar Alhamis da ta gabata.

A jiya Lahadi ne dai Sanusi Bature, mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Abba Kabir ya sanar da cewa gwamnan zai sake komawa jam’iyyar APC a yau Litinin.

A ranar Juma’a ne Abba Kabir ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP da aka zaɓe shi a karkashinta a shekarar 2023.

Gwamnan ya bayyana rikicin cikin gida da fifita ci gaban al’ummar jihar Kano a matsayin dalilansa na ficewa daga NNPP.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments