Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiMata da kananan yara na cikin wandada suka fi fuskantar cin zarafi...

Mata da kananan yara na cikin wandada suka fi fuskantar cin zarafi Sudan

Mata na daga cikin wadanda aka fi cin zarafinsu a yaƙin Sudan, inda suke fuskantar cin zarafi da sauran laifukan da aka aikata ba tare da an hukunta masu aikata hakan ba, in ji Sulaima Ishaq al-Khalifa wata mai fafutukar kare hakkin bil’Adama wacce ta zama ministar harkokin zamantakewa ta gwamnatin da ke samun goyon bayan sojojin Sudan.

Sojojin Sudan da rundunar sa kai ta RSF na fada da juna tun watan Afrilun 2023 – rikicin ya haddasa mutuwar mutane da dama da kuma raba mutane kusan miliyan 11 da muhallinsu, galibin su mata da yara.

Kungiyoyi daga cikin da wajen ƙasar ne ke kokawa ganin halin matsin da matan suke fuskanta.

Ƙungiyoyi masu dauke da makamai na barazana ga rayuwar mazauna karkara, musaman yankunan da ke fama da rashin abinci da dai sauran su musaman ababen more rayuwa, inda suke amfani da hakan domin cin zarafin mata – yara da manya.

Sulaima Ishaq al-Khalifa ta ce cin zarafin mata ya kan kasance tare da fashi da makami ta hanyar kai hari, tare da rahotannin fyade da azabtarwa da matan ke fuskanta.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments