Yan sandan Jihar Borno sun cafke wata mata mai shekaru 22 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a tashar mota ta Baga Road a garin Maiduguri, tare da kwato fakiti 89 na tramadol.
Hakan dai na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar a ranar Asabar 24 ga watan Janairu na shekarar 2026.
Sanarwar ta ce an cafke matar ne bayan bayanan sirri da ’yan sanda suka samu, inda suka tare ta a tashar motar Baga Road.
Sanarwar ta bayyana cewa an samu matar da wani buhu ɗauke da garin masara, wanda aka ɓoye fakiti 89 na maganin tramadol a cikinsa, yayin da take shirin aikewa da kayan zuwa Karamar Hukumar Damasak.
Sanarwar ta ƙara da cewa binciken farko ya nuna an ba ta saƙon kai buhun, kuma ana ci gaba da bincike tare da neman sauran mutanen da ake zargi da hannu a lamarin.