Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiSojoji sun yi nasarar kashe Shugaban yan ta’adda tare da kama wasu...

Sojoji sun yi nasarar kashe Shugaban yan ta’adda tare da kama wasu 34 a Borno

Hedkwatar Tsaro DHQ ta ce sojoji sun kashe wani kwamandan ‘yan ta’adda, Munzir wanda aka fi sani da Baa Yanziye, tare da wasu da dama a lokacin hare-haren sama da kuma kama ‘yan ta’adda 34 a cikin makonni biyu da suka gabata a yankin Arewa maso Gabas.

Daraktan Ayyukan Watsa Labarai na Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce wani kwamandan ‘yan ta’adda mai suna Yakubu Adamu ya mika wuya ga sojoji da makamansa da harsasai a yankin Azir Wajiroko.

Ya ce sojoji tsakanin 1 ga Janairu zuwa 15, 2026, sun gudanar da ayyuka kan ‘yan ta’adda a kananan hukumomin Gwoza, Konduga, Bama da Damboa na Jihar Borno.

Har ila yau, sojojin sun kuma ci gaba da kai samame a sauran yankunan da suka hada da Askira Uba, Chibok, Mafa da Guzamala a jihar.

Ya kara da cewa, sojoji a lokacin fafatawar sun kashe ‘yan ta’adda da dama, sun kama 34 sannan sun ceto mutane 17 da aka yi garkuwa da su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments