Tawagar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ta yi nasarar haura wa zuwa matsayi na 26 a jadawalin iya taka leda a kwallon kafa da hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) ta fitar.
Wannan na zuwa ne bayan kokarin da Super Eagles ta yi a gasar da aka kammala a kasar Morocco inda suka kare a matsayi na uku.
Tawagar, karkashin jagorancin Koci Eric Chelle, ta samu nasara shida, inda ta yi rashin nasara sau daya kacal a wasanni bakwai da ta buga a gasar AFCON ta bana.
Super Eagles ta samu maki 1581.55 a watan Janairun 2026, inda ta samu karin maki 79 daga maki 1502.46 da take dashi a watan Disamban 2025.
A yanzu Super Eagles ke zaune a matsayi na 3 a iya taka leda a nahiyar Afrika, wanda ke nufin ta sha gaban kasar Algeria a jadawalin, kasashen Morocco da Senegal ne kadai ke saman Nijeriya a sabon jadawalin da FIFA ta fitar.
Duk da rashin nasara a wasan karshe na gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirika da Morocco ta yi, amma ta cigaba da rike matsayinta na daya a nahiyar Afrika a 7 inda take matsayi na takwas a jadawalin duniya.
Senegal da take matsayi na 2 a nahiyar Afrika ta samu nasarar zama ta 12 a jadawalin duniya.