Wasu fusatattun matasa da ke zanga-zanga a jihar Edo ta Kudu maso Kudancin Najeriya sun afkawa kasuwar sayar da dabbobi ta ƴan Arewa da ke ƙaramar hukumar Ekpoma ta jihar inda suka sace dukiya mai tarin yawa tare da jikkata wasu ƴan kasuwar Arewacin ƙasar da ke tsaka da hada-hadarsu.
Rahotanni sun bayyana cewa, tun bayan isar su kasuwar, masu zanga-zangar sun ɓarnata dukiyoyin jama’a a kan hanya waɗanda suka haɗa da farmakar gidan basaraken yankin, baya ga shagunan gefen gari.
Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa ƴan Arewa ne ke haifar da matsalolin tsaro a jihar sai dai bayanai na nuni da cewa har kawo yanzu ba a taɓa samun wani ɗan Arewa ko kuma bahaushe da laifin ta’addancin ba.
Ko a bara sai da wasu jami’an tsaro na jihar ta Edo suka kashe Mafarautan jihar Kano 14 ta hanyar banka musu wuta da ransu bayan zarginsu da kasancewa ƴan bindiga duk kuwa da irin bayanin da suka riƙa yi musu, ba kuma tare da miƙa su ga ƴansanda don bincikarsu ba.