Sunday, October 18, 2026
HomeWasanniA yau ne a za a ci gaba da fatawa a wasan...

A yau ne a za a ci gaba da fatawa a wasan cin kofin AFCON

Yau ake dawowa domin ci gaba da fafata wasanin gasar cin kofin Afirka da ke gudana a kasar Morocco, yayin da za a doka matakin dab da karshe wato semi-final tsakanin ƙasashe hudu da suka rage.

Wasa na farko dai zai gudana ne da misalin karfe 6 na yamma agogon Nijar da Kamaru, shi ne fafatawa tsakanin Senegal da Masar da ke neman kofin karo na 8.

Sai dai wasan da zai fi daukar hankali shi ne, fafatawar da Najeriya za ta yi da Moroko mai masaukin baki a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke birnin Rabat, da misalin ƙarfe 9, la’akari da yadda suke taka rawar gani a baya-bayanan.

Super Eagles dai na fatan lashe kambin Afrika karo na huɗu jimilla,wanda rabonta da shi tun shekarar 2013, Moroko kuwa na neman kofin karo na biyu, kari kan wanda ta ɗauka a shekarar 1976.

Dukkan tawagogin biyu ba su yi rashin nasara ba tun daga farkon wannan gasar, sai dai Najeriya ta lashe dukkan wasannin biyar da ta doka, yayin da Morocco ta yi nasara huɗu.

Wannan ita ce haduwa ta 6 tsakaninsu a AFCON kuma kowanne daga ciki ana samun wacce kan doke wata a tsakaninsu, wato kunnnen doki, haduwarsu ta karshe tun shekarar 2004, wato shekaru 22 da suka wuce.

kuma wannan itace haduwarsu ta biyu a zagayen daf da na ƙarshe a AFCON.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments