Sojoji sun kai hare-hare kan ’yan ta’adda a sassa daban-daban na Jihar Borno, inda suka kashe wasu, wasu kuma suka miƙa wuya tare da kwato makamai da kayan aiki.
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan na cikin sanarwar da Rundunar Operation Hadin Kai ta fitar a ranar Lahadi 11 ga Janairu, 2026.
Sanarwar ta ce matsin lamba da sojoji suka yi a yankin Azir zuwa Wajiroko ya tilasta wa ’yan ta’adda 11 miƙa wuya tare da bindigogin AK-47 da harsasai, yayin da a wasu samame aka kashe ’yan ta’adda takwas.
Sanarwar ta ƙara da cewa an lalata sansanonin ’yan ta’adda a wasu yankunan jihar, tare da kama mutane biyu da ake zargi da taimaka musu da kayan aiki a Karamar Hukumar Gubio.