Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa ana tattaunawa tsakaninta da jam’iyyun NNPP da PDP kan yiwuwar haɗaka gabanin zaɓen 2027 mai zuwa.
Alamu na ƙara bayyana cewa wasu jam’iyyun siyasa a Najeriya na nazarin sake haduwa gabanin zaɓen shekarar 2027, da nufin kalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyarsa ta APC.
Wannan yunƙuri na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta tattaunawa a bayan fage tsakanin manyan jam’iyyun adawa a fadin Najeriya.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana maganar hadakar a Abuja, inda ya ce jam’iyyarsa na tattaunawa da NNPP da PDP domin duba yiwuwar kafa wata haɗaka.
A cewarsa, manufar tattaunawar ita ce samar da tsari da zai kawo sauƙi da kyakkyawar rayuwa ga al’ummar Najeriya, musamman duba da halin da ƙasar ke ciki a fannoni da dama.
Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa tattaunawar da ake yi tsakanin ADC, NNPP da PDP na ci gaba, inda kowace jam’iyya ke bayyana matsayinta kan yadda za a gina haɗakar da za ta kasance mai fa’ida ga jama’a.
Ya jaddada cewa abin da jam’iyyun ke dubawa shi ne yadda za a samar da shugabanci nagari, da manufofi masu ma’ana da za su inganta rayuwar talakawa.
Bolaji Abdullahi ya kuma bayyana cewa ADC na ƙoƙarin gina jam’iyya mai ƙarfi da tsarin dimokuraɗiyya na gaskiya, inda ra’ayin mambobi zai zama ginshiƙi a yanke manyan shawarwari.