Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 6.14 domin tafiye-tafiyen kasashen waje na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a cikin daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026.
Bisa ga kasafin da aka gabatar, an kara Naira miliyan 873.88 domin tafiye-tafiye na cikin gida, wanda ya kai jimillar kuɗin tafiye-tafiyen Shugaba Tinubu zuwa Naira biliyan 7.01.
Rahotanni sun bayyana cewa ga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, kasafin ya tanadi Naira biliyan 1.73 domin tafiye-tafiye da harkokin sufuri.
Shettima zai lashe biliyoyi don tafiye-tafiye , wanda ya haɗa da Naira miliyan 417.48 na tafiye-tafiye na cikin gida da kuma Naira biliyan 1.31 na zuwa zuwa kasashen waje.
Takardun kasafin sun nuna cewa kuɗaɗen tafiye-tafiyen kasashen waje na shugaban kasa da mataimakinsa suna karkashin sashen ayyukan fadar shugaban kasa.
Jimillar kuɗin da aka ware a wannan sashe sun haɗa da Naira biliyan 8.38 don ayyukan fadar shugaban kasa, da kuma Naira biliyan 2.64 don ayyukan fadar mataimakin shugaban kasa a kasafin 2026.