Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiZa mu riƙa karɓar gangar mai kimanin miliyan 50 daga Venezuela -...

Za mu riƙa karɓar gangar mai kimanin miliyan 50 daga Venezuela – Trump

Trump ya bayyana cewa kasar Amurka zata rika karbar gangar mai Miliyan 50 a Venezuela

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce hukumomin riƙon-ƙwarya na Venezuela za su rika ba wa Amurkar, gangar mai tsakanin miliyan 30 zuwa 50 na abin da ya kira man da aka sanya wa takunkumi.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce za a riƙa sayar da man ne a farashin kasuwa – sannan kuma shi zai sarrafa kuɗin inda ya ce, kudin zai amfani al’ummar Venezuela da kuma Amurka.

Hukumomin Venezuelar dai ba su tabbatar da wannan shiri ba.
Tun da farko, shugabar rikon kwarya ta Venezuelar, Delcy Rodriguez, ta ce babu wani dan ƙasar waje da ke mulkin kasarta.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments