Aƙalla yara 469 ne suka mutu sakamakon matsalolin rashin abinci mai gina jiki a Jihar Kano tsakanin watan Janairu da Yuli na shekarar 2025.
Farfesa Ruqayya Yusuf daga Sashen Ilimin yada labarai da sadarwa ta jami’ar Bayero ce ta bayyana hakan yayin wani taron wayar da kan ‘yan jarida kan hanyoyin da za a bi wajen yaƙar matsalar rashin gina jiki a jihar.
Ta ce rashin abinci mai gina jiki da kuma munanan dabi’un ciyarwa na ci gaba da zama babbar barazana ga lafiyar al’umma a Kano, duk da matakan da ake ɗauka.
Farfesa Ruqayya ta kara da cewa Najeriya na ci gaba da samun matsayi mara kyau a ma’aunin lafiyar abinci na duniya.
Ta ambato rahoton UNICEF na 2025, da ya ace kusan kashi 40 cikin 100 na yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar a Najeriya na fama da rashin girma yadda ya kamata, yayin da lamarin ya fi muni a Kano, inda kusan kashi 51.9 cikin 100 na yara ke fama da matsalar tsaikon girma.
Ta bayyana cewa talauci, rashin wadataccen abinci, munanan dabi’un ciyarwa, da kuma ƙarancin bayanan kiwon lafiya ne ke haddasa yawaitar matsalar.
Haka kuma, wata masaniyar harkar amfanin gona, Amina Ado-Yahaya, ta ce Jihar Kano ce ke da mafi yawan yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar masu ƙarancin nauyi a Najeriya, wanda ya kai kusan kashi 42.6 cikin 100.
Ta yi kira da a rungumi hanyoyin cikin gida kamar noman kayan lambu a gidaje domin inganta lafiyar abinci a matakin iyali.
Ta kuma yi gargaɗi cewa ƙarancin bitamin A na ci gaba da zama babbar matsalar lafiyar jama’a, tana mai cewa hakan na haddasa makantar yara tare da tsananta cututtuka irin su kyanda da gudawa.
Masana sun yi kira ga gwamnati, kafafen yaɗa labarai, al’umma da kuma abokan hulɗar ci gaba da su haɗa kai domin shawo kan matsalar rashin gina jiki da ke ƙara ta’azzara a Jihar Kano.