Alkali mai shari’a Justice Emeka Nwite na Federal High Court Abuja ya bayar da belin tsohon Ministan Shari’ah Abubakar Malami, SAN tare da matarsa da dansa akan kudi Naira Miliyan dari biyar.
A cewar alƙalin, mutanen da za su tsaya musu sai sun kasance suna da filaye a yankunan Asokoro da Maitama ko Gwarinpa, sannan kuma sai sun miƙa dukkan takardun tafiyarsu ga kotu.
Kwanakin baya ne dai hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta gabatar da tuhume-tuhume 16 a kan Malami da iyalinsa masu alaƙala da halasta kuɗaɗen haram da kuma mallakar kadarori da darajarsu ta haura naira biliyan 8.7 wanda ya kai ga tsaresu a gidan yarin Kuje da ke Abuja.