Dandazon magoya bayan shugaban Venezuela, Nicolás Maduro, sun mamaye titunan babban birnin ƙasar Caracas, suna nuna fushinsu kan kama shi da Amurka ta yi tare da buƙatar a dawo da shi gida.
Magoya bayan shugaban sun ce matakin da Amurka ta ɗauka ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.
Magoya bayan gwamnatin, musamman masu ra’ayin neman sauyi, sun bayyana cewa har yanzu suna cike da ɓacin rai kan abin da suka kira tsoma bakin Amurka a harkokin cikin gidan Venezuela a ƙarshen mako.
A yayin sauraron ƙarar da ake yi masa a wani kotu a birnin New York, Nicolás Maduro ya jaddada cewa har yanzu shi ne halastaccen shugaban Venezuela inda ya bayyana kama shi da sojojin Amurka suka yi a ranar Asabar a matsayin “sace shi”.
Maduro da matarsa, Cilia Flores, wadda ita ma aka kama, sun musanta dukkan tuhumar da ake yi musu ta laifukan hada-hadar miyagun ƙwayoyi da ta’addanci.
A halin yanzu, an rantsar da mataimakiyarsa a matsayin shugabar riko ta Venezuela, yayin da rikicin siyasar ƙasar ke kara kamari.