Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaAPC ta neman Nyesom Wike ya ajiye muƙamin Ministan Abuja

APC ta neman Nyesom Wike ya ajiye muƙamin Ministan Abuja

Zazzafar cacar-baki ta kaure tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike, da Sakataren Jam’iyyar APC, Ajibola Bashiru, lamarin da ya kai ga sakataren jam’iyyar kiran Wike ya sauka daga muƙaminsa na minista, bisa hujjar cewa ba ɗan jam’iyyar APC ba ne.

Lamarin na zuwa ne bayan Wike ya gargaɗi sakataren ya tsame hannunsa daga siyasar jihar Ribas, saboda sanarwar da APC ta fitar cewa Gwamna Siminalayi Fubara ne jagora kuma shugaban jam’iyyar mai mulki a jihar.

Rikicin ya faro ne tun bayan ziyarar da sakataren APC da tawagarsa suka kai wa Gwamna Siminalayi Fubara a jihar Ribas, inda daga bisani Bashiru ya sake jaddada tsarin jam’iyyar cewa kowane gwamna shi ne jagoran jam’iyyar a jiharsa.

Sakataren ya ce Nyesom Wike ba ɗan APC ba ne, don haka ba shi da hurumin tsoma baki a harkokin jam’iyyar, tare da shawartarsa da ya sauka daga muƙamin minista kuma ya daina halartar taron Majalisar Zartarwar ƙasar.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments