Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya musanta wani labari da ke yawo wanda ke cewa ya ce Amurka na son kai masa hari domin kawar da shi
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Gumi ya bayyana labarin a matsayin tsagwaron ƙarya, yana mai cewa bai taɓa faɗin haka ba, kuma bai taɓa tunanin hakan zai faru ba
Ya bayyana cewa an samu saɓanin fahimta ne daga wani wa’azi da ya yi a masallaci, inda ya ba da labarin wani tsohon lamari na barazanar tsaro da ya shafi ƙungiyar Boko Haram.
Sheikh Gumi ya ce a watan Agustan 2012 aka sanar da shi cewa ƙungiyar Boko Haram ta shirya kashe shi, amma ba a yi nasara ba, bayan da mutanen da aka aiko suka mutu sakamakon fashewar bam ɗin da suke ɗauke da shi a kusa da gidansa.
Malamin ya jaddada cewa a halin yanzu yana zaune lafiya tare da iyalansa, ba tare da tsoro ko fargaba ba.
Ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da suka wallafa labarin da su gyara kuskuren tare da ba da haƙuri ga jama’a.