Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya ba hukumomin tsaro umarnin kamo maharan Neja

Tinubu ya ba hukumomin tsaro umarnin kamo maharan Neja

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya umarci Ministan tsaron ƙasar da Babban Hafsan Tsaron ƙasar da manyan hafsoshin sojin ƙasar da babban Sufeton ƴan sanda da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya su farauto tare da kama maharan Kasuwan Daji da ke jihar Neja, domin su fuskanci hukunci.

A ranar Asabar da maraice ne dai wasu mahara suka far wa ƙauyen Kasuwan Daji a jihar Neja inda suka kashe fiye da mutum 30 tare da sace wasu mata da ƙananan yara da ba a san adadinsu ba da kuma ƙona kasuwar da sace kayan abinci.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya umarci jami’an tsaron ƙasar su kuɓutar da mutanen da maharan suka sace.

Sanarwar ta ce ana zargin maharan sun taso ne daga jihohin Sokoto da Zamfara domin guje wa hare-haren da Amurka ta kai musu a jajiberin Kirsimeti.

Haka kuma Tinubu ya ba da saƙon ta’aziyya ga iyalan mutanen da harin ya rutsa da su.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments