Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaAn tsaurara matakan tsaro a gidan Gwamnatin Kano

An tsaurara matakan tsaro a gidan Gwamnatin Kano

Biyo bayan shirin sauya sekar Abba Kabir Yusuf zuwa APC an kara tsaurara matakan tsaro

An ƙara tsaurara matakan tsaro a kewaye da ciki Gidan Gwamnatin Jihar Kano, sakamakon shirin Gwamna Abba Yusuf na sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

tarin jami’an tsaro a kewayen da kuma cikin Gidan Gwamnatin Kano, bayan shirin sauya sheƙar gwamnan zuwa jam’iyyar APC.

DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa tura jami’an tsaro na zuwa ne yayin da shirin sauya sheƙar gwamnan ke fuskantar tsananin adawa, musamman daga bangaren Kwankwasiyya.

A cewar majiyoyin tsaro, an ɗauki wannan mataki ne domin hana yiwuwar ɓarkewar rikice-rikice da karya doka da oda a jihar.

“Babu shakka wannan mataki ya tayar da hankalin da dama daga cikin magoya bayan gwamnan da kuma mambobin tafiyar Kwankwasiyya. Gwamnan na fuskantar ƙalubale sosai,” in ji majiyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments