Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, zai sauya sheƙa a hukumance zuwa jam’iyyar mai mulki ta APC a ranar Litinin, kamar yadda jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda shi kaɗai ne gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, ya riga ya isa Abuja domin kammala shirye-shiryen sauya sheƙarsa.
Majiyoyi sun bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Yitwalda Nentawe, ne za su karɓi gwamnan an Abuja.
Tuni dai an kira shugaban jam’iyyar APC a Kano, Abdullahi Ganduje, daga tafiyar da yake yi a Dubai, haka nan kuma an bukaci shugaban jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas, da ya dawo gida daga tafiyar Umrah da yake yi domin ba gwamnan katin zama ɗan APC a mazabarsa ta Diso da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano a cikin makon nan.