Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiƳan sanda sun janye dokar kama motoci masu gilashi mai duhu

Ƴan sanda sun janye dokar kama motoci masu gilashi mai duhu

Yan sanda sun dakatar da dokar sanya gilashin mota mai duhu

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta sanar da dakatar da kamen motoci masu gilashi mai duhu a faɗin ƙasar, biyo bayan umarnin kotu na wucin-gadi da ya hana aiwatar da dokar.

A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, rundunar ta ce matakin dakatarwar ya biyo bayan ƙarar da ke gaban kotu, inda aka umurci rundunar ta dakata da aiwatar da dokar har sai an yanke hukunci.

Tun a ranar 15 ga Disamba, 2025 ne rundunar ta bayyana aniyarta ta fara aiwatar da dokar mallakar lasisin amfani da gilashin mota mai duhu daga ranar 2 ga Janairu, 2026, tana mai cewa hakan na da nufin ƙarfafa tsaro da kare lafiyar jama’a.

Sai dai a wata sanarwa da kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin ya fitar, ya ce an miƙa wa rundunar umarnin kotu a ranar 17 ga Disamba, 2025, wanda ya hana ci gaba da aiwatar da dokar.

Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar ta riga ta bayyana a gaban kotu, ta gabatar da ƙorafe-ƙorafen farko tare da neman kotun ta janye umarnin dakatarwar.

An ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 20 ga Janairun 2026 domin ci gaba da shari’a, yayin da dokar za ta ci gaba da kasancewa a dakace har sai kotu ta yanke hukunci ko ta janye umarnin.

Rundunar ta kuma tabbatar wa al’umma cewa za ta sanar da su duk wani sabon mataki ko bayani bayan hukuncin kotu, domin kiyaye zaman lafiya da tsaron ƙasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments