Wasu alƙaluma da cibiyar ƴan jaridu ta ƙasa da ƙasa wato IFJ ta fitar ta ce akwai ƴan jarida har 128 da aka kashe cikin shekarar da ta gabata a sassan daban-daban na duniya da kaso mai yawa a Gabas ta Tsakiya.
Sakatare Janar na IFJ Anthony Bellanger ya ce adadin ya ƙaru daga yawan ƴan jaridan da aka kashe a shekarar 2024 wanda ke nuna matuƙar haɗarin da ma’aikatan na ɓangaren samowa da kuma yaɗa labarai ke fuskanta a sassan daban-daban na duniya.
IFJ ta ce a Gaza kaɗai Isra’ila ta kashe ƴan jarida 56 a shekarar ta 2025 wanda ke nuna buƙatar ganin ƙasashe su mutunta ƴan jarida da ma aikin da suke gudanarwa.
Ƙungiyar ta kuma cewa hallau akwai tarin ƴan jarida da aka kashe a ƙasashe irin Yemen da Sudan da Ukraine da Peru da kuma India.
Cibiyar ta IFJ ta ce ƴan jarida na buƙatar cikakkiyar kariya a yayin aikinsu a dukkan matakai, sai dai abin takaice ne galibi matsalolin kan ƙare a kansu da zarar wata rigima ta taso.
Bellanger ya ce duk da kasancewar ƴan jarida ba masu ɗaukar ɓangare ba, amma ɓangarorin da ke rikici da juna kan nuface kai tsaye don cutar da su.