Yan wasan Super Eagles sun doke Tiafa Stars na Tanzania da ci 2 da 1 a wasansu na farko da suka buga karkashin gasar cin kofin duniya na shekarar nan ta 2025.
An fara gudanar da wasan cikin karsashi inda Najeriya ke kan gaba, duk kuwa da cewa a lokuta da dama Tanzanian ta yi barazanar haye ta.
A mintuna 36 da fara wasan Najeriya ta jefa kwallonta na farko a raga, sai dai da dawo wa daga hutun rabin lokaci Tanzanian ta fanshe, wato mintina 2 da dawowa ɗan wasan tsakiya na Tanzanian Charles M’Mombwa ya zura ƙwallo a ragar sakamakon saken da ƴan wasan Najeriyar suka yi a wannan lokaci, lamarin da ya matukar tayar da hankalinsu.
Amma ana shiga mintina 55 da yin wasa, cikin salo mai daukar hankali ɗan wasa Ademola Lookman ya zurawa Najeriyar kwallonta na biyu.
Daga bisani kuma Tanzanian ta yi duk mai yiwuwa wajen ƙwace nasarar daga Najeriyar amma yan wasan su ka yi tirjiya wajen hana faruwar hakan, wato basu sake ci ba, sannan basu bari Tazanian ta sake zura wani kwallon ba.