Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaINEC yi watsi da Tanimu Turaki a matsayin shugaban PDP

INEC yi watsi da Tanimu Turaki a matsayin shugaban PDP

Hukumar INEC taki amincewa da Aminu Turaki a matsayin Shugaban PDP

Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta, INEC ta ce ba za ta amince da Kabiru Tanimu Turaki a matsayin shugaban jam’iyyar PDP ba.

Ta ce ta yi hakan ne bisa amfani da shari’o’i da ke kotu.

Wannan dai na ɗauke ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan watan 22 ga watan Disamba da sakataren hukumar, Dakta Rose Oriaran-Anthony ya sakawa hannu wadda jaridar Punch ta samu.

INEC ta ce ta ɗauki wannan matakin ne bayan wasiƙu da ta samu daga lauyoyin jam’iyyar PDP cewa ta gyaran bayanan jam’iyyar da ke rumbun bayananta dangane da sunayen shugagannin jam’iyyun na ƙasa da aka zaɓa a babban taron jam’iyyar a jihar Oyo a watan Nuwamban da ya gabata.

Hukumar INEC ta ce ta yi duba da nazari kan buƙatun lauyoyin bisa dogaro da “abin da yake na gaskiya, da dokoki da kuma hukunce-hukuncen kotuna dangane da batun”, da suka hana hukumar sa ido ko kuma amince wa da sakamakon abin da ya fito daga taron na ranar 15 ga watan Nuwamba, 2025.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments