Pakistan ta cimma yarjejeniyar sayar wa Sojin Libya da makamai da suka haura Dala biliyan 4, a cewar wasu jami’an Sojin ƙasar duk da takunkumin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta dorawa ƙasar da ke fama da matsalar tsaro .
Wannan yarjejeniyar na daga cikin manyan cinikayyar kasuwanci na makamai da Pakistan ta cimma da wata ƙasa a wani zaman tattaunawar da ya gudana a makon jiya ƙarƙashin jagorancin Field Marshal Asim Munir da Saddam Khalifa Haftar,mataimakin babban kwamandan Sojin Libya da ke Bengahazi a gabanshin Libya.
Sai dai wasu daga cikin masu faɗa aji a tattaunawar sun ƙi amincewa su bayyana kansu, daga cikinsu har da ministan harkokin wajen Pakistan da ma’aikatar tsaron ƙasar la’akari da girman maganar.
Cinikin makamai zai iya gamuwa da cikas saboda rashin tsayayyar gwamnati a Libya tun bayan kifar da Shugabancin Muammar Gaddafi, a shekarar 2011.