Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeAmurka ta ƙulla yarjejeniya da Najeriya kan kyautata kiwon lafiyar Kiristoci

Amurka ta ƙulla yarjejeniya da Najeriya kan kyautata kiwon lafiyar Kiristoci

Kasar Amurka ta kulla yarjejeniya da Najeriya kan kyautata lafiyar Kiristoci

Amurka ta ƙulla yarjejeniya da Najeriya don mayar da hankali kan kyautata kiwon lafiyar Kiristoci.

Amurka ta sanar da cewa ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya don ƙarfafa tsarin kiwon lafiya na
Najeriya, ‘yan makonni bayan Shugaba Donald Trump ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.

A watan da ya gabata, Trump ya ce Amurka ta shirya kai hari Najeriya domin kawar da masu yi wa “Kiristoci kisan gilla.”

A ƙarƙashin yarjejeniya ta shekaru biyar da aka ƙulla a yanzu, Washington za ta bayar da kusan Dala biliyan 2.1 don taimakawa wajen hana yaɗuwar HIV, tarin fuka, zazzaɓin cizon sauro da cutar shan inna, da kuma kare lafiyar mata masu juna biyu da yara, in ji wani mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka a ranar Asabar.

Najeriya ta yi alƙawarin kashe ƙarin kusan Dala biliyan 3 a cikin shekaru biyar masu zuwa, in ji kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, yana mai ƙarawa da cewa yarjejeniyar ta ƙunshi “mayar da hankali kan tallafa wa cibiyoyin kiwon lafiya masu alaƙa da addinin Kiristanci.”

Shugaban Amurka ya ce Kiristanci na fuskantar “barazana ta gushewa” daga Najeriya da “ƙasashe da dama,” yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta bari a ci gaba da tsangwamar Kiristoci ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments