Hukumar da ke kula da harkokin addini a Masarautar Sakkwato ta sanar da Musulmi a fadin Najeriya cewa za a fara duba watan Rajab na 1447AH a yau Asabar, 20, Disamba, 2025.
A cewar sanarwar, ranar da aka kayyade ta yi daidai da 29 ga watan Jumada Assaniya 1447AH.
An bukaci Musulmi da su mayar da hankali wajen duba watan da zarar rana ta fadi, tare da tabbatar da sahihancin abin da suka gani.
Rajab, shi ne wata na bakwai a kalandar Musulunci daga shi kuma sai Sha’aban, sannan Ramadan da Musulmi ke azumi a cikinsa.
Sanarwar da fadar Sarkin Musulmi ta fitar a Facebook ta jaddada cewa duk wanda ya ga wata, wajibi ne ya bi hanyar da aka saba domin kai rahoto ga mahukunta.