Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiShugaba Tinubu ya gargaɗi gwamnoni kan kudin kananan hukumomi

Shugaba Tinubu ya gargaɗi gwamnoni kan kudin kananan hukumomi

Tinubu ya gargadi gwamnoni kan batun kudin kananan hukumomi.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi gwamnonin jihohi kan kudin kananan hukumomi.

Tinubu ya gargadi gwamnonin cewa zai iya bayar da umarni domin tilasta biyan kudin kananan hukumomi kai tsaye idan suka ƙi bin hukuncin Kotun Koli.

Tinubu ya kuma bukaci gwamnonin su aiwatar da hukuncin Kotun Koli wanda ya umarci a sakarwa kananan hukumomi mara.

Shugaban kasar ya fito kai tsaye ya gayawa gwamnonin matakin da zai dauka idan har ba su aiwatar da hakan ba.

​Shugaban kasar ya sake yin wannan gargaɗi ne a ranar Juma’a, 19 ga watan Disamban 2025, yayin da yake jawabi a taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 15 na jam’iyyar APC.

An gudanar da taron ne a dakin taro na fadar shugaban kasa, da ke birnin Abuja.

Tinubu ya ce rashin bin hukuncin kotu kan ‘yancin kananan hukumomi na iya tilasta masa tabbatar da cewa ana biyansu kudin kai tsaye daga asusun rarraba kudi na tarayya (FAAC).

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments