Babban Hafson Sojin Pakistan, Asim Munir ya shiga tsaka mai wuya bayan da Donald Trump ya miƙawa Islamabad buƙatar bayar da dakaru don taimakawa wajen samar da runduna ta musamman a Gaza, matakin da masu sharhi ke ganin ka iya zama babban ƙalubale ga matsayar ƙasar ta fannin siyasar duniya.
Bayanai sun bayyana cewa a makon gobe Munir ke shirin balaguro zuwa Amurka don ganawa da Trump wacce za ta zama ganawa ta 3 cikin watanni 6 tsakanin shi da Trump, inda ake sa ran za su tattauna a kan makomar Gaza a wani yanayi da Amurka ke son tattaro dakaru daga ƙasashen Musulmi waɗanda Isra’ila ta amince da sahihancinsu don girke su a Gaza.
Sai dai wasu ƙasashen na kallon matakin a wani yunƙuri na shigar da su yaƙin a kaikaice ko kuma amfani da salon wajen zargarsu da taimakawa ayyukan ta’addanci da ka iya taɓa ƙimarsu ganin yadda Amurkan da Isra’ila suka ƙi amincewa da wasu ƙasashe waɗanda a raɗin kansu suka miƙa buƙatar bayar da dakarun don zama a Gaza.
Ƙarƙashin yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin Isra’ila da mayaƙan Hamas na Gaza bisa jagorancin Amurka, an tanadi girke dakarun ƙasashe a Gaza don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a yankin sai dai har yanzu ba a kai ga tantance adadin ƙasashen da zasu girke dakarun ba.
Donald Trump da kan shi ke bibiyar ƙasashe wajen ganin sun amince da buƙatar shi ta aikewa da dakarun, sai dai da dama daga cikin ƙasashen musulmin na ɗari – ɗari saboda fargabar abin da zai biyo baya.
Tun farko wasu ƙsashen sun miƙa buƙatar girke dakarun amma Amurka da Isra’ila sun ƙi amincewa ciki har da Turkiya, yayin da a gefe guda Indonesia itama ta yi tayin aikewa da dakarun soji dubu 20.