Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAmurka na kokarin mayar da ƙasata ƙarƙashin mulkin mallaka – Venezuela

Amurka na kokarin mayar da ƙasata ƙarƙashin mulkin mallaka – Venezuela

Shugaban Kasar Venezuela ya zargi Amurka da neman kasar sa karkashin mulkin mallaka.

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro, ya zargi Amurka da neman mayar da ƙasarsa karkashin mulkin mallaka.

Shugaban nanata cewa kasarsa ba za ta zama karkashin mulkin mallakar wani ko wata kasa ba har abada.

A cikin wani jawabi da ya gabatar na nuna turjiya, ya ce duk wani yunkuri na hamɓarar da gwamnatinsa ba zai yi wani tasiri ba.

Kalamansa na zuwa ne kwana guda bayan shugaba Trump ya sanar da dakatarwa da kuma sanya takunkumi a kan wasu tankokin dakon mai, yana mai cewa yanzu Venezuela na kewaye da sojojin Amurka.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta buƙaci ɓangarorin biyu da su daina rura wutar rikicin, sannan kuma shugabar Mexico, Claudia Sheinbaum, ta yi kira da a zauna a tattauna domin kare zubar da jini.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments