Wasu manyan ‘yan siyasar adawa sun gargadi Shugaban Kasa, Bola Tinubu gargadi a kan zargin shirin mayar da Najeriya ta koma ƙasar jam’iyya ɗaya tak.
Sun zargi jam’iyyar APC da amfani da hukumomin tsaro da na yaƙi da cin hanci wajen tsoratar da ‘yan adawa, musamman kafin zaɓen 2027. A cewarsu, wannan abu na barazana ga dimokuraɗiyyar ƙasar.
A wata sanarwa da suka fitar tare, ‘yan adawar sun ce sun damu matuƙa da yadda ake amfani da hukumomin gwamnati wajen matsa wa ‘yan adawa ba tare da dalili ba. Sun ce hakan na rage yarda da hukumomin ƙasa a idon jama’a.
Sanarwar ta samu sa hannun manyan mutane irin su tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark, da Peter Obi na jam’iyyar Labour. Haka kuma akwai Cif Bode George, Cif John Odigie-Oyegun da Mallam Lawal Batagarawa.
Yan adawa na zargin APC da rike wa gwamnonin adawa wuta
‘Yan adawar sun ce akwai wani shirin ɓoye na tilasta dukkannin jihohi su koma ƙarƙashin jam’iyya mai mulki, ba ta hanyar sahihin zaɓe ba, sai dai ta hanyar matsin lamba da binciken cin hanci.
Sun ce sauya sheƙar wasu gwamnonin adawa zuwa APC a baya-bayan nan ya sa mutane da dama ke tunanin an tilasta musu hakan, ba wai sun sauya ra’ayi da yardar kansu ba.
A cewarsu, matsalar ba gwamnonin kaɗai ta shafa ba, har da manyan ‘yan adawa da ke shirin haɗin gwiwa domin zaɓen 2027.
Sun kuma zargi hukumar EFCC da yin aiki bisa tasirin siyasa, inda ake watsi da zargin da ya shafi ‘yan jam’iyya mai mulki, amma ana hanzarta bincike da fallasa ‘yan adawa a kafafen watsa labarai.
‘Yan adawar sun yi gargaɗi cewa irin wannan hali na lalata amincewa da yaƙi da cin hanci, yana raunana hukumomi, kuma na iya haddasa rikici yayin da zaɓe ke ƙara matsowa kusa.