Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya tabbatar da cewa wani hari ta jirgi mara matuƙi ya kai farmaki kan wata cibiyar Majalisar a Sudan, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami’an.
A cewar sanarwar, makamin ya sauka ne a kan sansanin kayan aiki na rundunar wanzar da zaman lafiya a birnin Kadugli, da ke yankin Kordofan ta Tsakiya.
Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an wanzar da zaman lafiya takwas sun jikkata a harin kuma dukkan waɗanda abin ya shafa ƴan ƙasar Bangladesh ne.
Babban sakataren Antonio Guterres wanda ya yi kakkausar suka kan harin, ya ce kai hari kan jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya abu ne mai matuƙar muni, tare da jaddada cewa irin waɗannan hare-hare na iya zama laifin yaƙi a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.
Ya ƙara da cewa babu wani dalili da zai kare wannan hari, yana mai jaddada cewa dole ne a tabbatar da ɗaukar mataki kan duk wanda ke da hannu a harin.
Rundunar sojin Sudan ta zargi Rundunar RSF, wata ƙungiyar sojojin sa-kai, da kai harin, sai dai har yanzu RSF ba ta mayar da martani kan zargin ba.
Rundunar sojin Sudan da RSF na fafatawa a yaƙin basasa da ya shafe sama da shekaru biyu.