Firaministan ƙasar, Anthony Albanese ya bayyana dokar ne a matsayin abin alfahari ga Australia, ya kuma bayyana hakan da muhimmin sauyi.
Anthony Albanese ya ce ƙasarsa na kan gaba a duniya wajen ɗaukar wannan mataki.
Yara ƙasa da shekaru 16 sun tarar an rufe musu shafukansu a manyan dandanli 10 ciki har da TikTok da Snapchat.
Sai dai ko a rana ta farko, rahotanni sun nuna cewa da dama daga cikinsu suna samun hanyoyin kaucewa wannan dokar.
Kamfanin Meta, mammallakin Instagram da Facebook, ya ce dokar na tura yara zuwa wasu shafuka da ba su da tsauraran dokoki.