Rundunar sojin saman Najeriya ta ce jami’anta suna cikin aminci kuma sun samu tarba mai kyau a Burkina Faso, sai dai kuma ƙungiyar AES ta ce duk wani jirgin da ya keta alfarmar sararin samaniyarta za a yi kaca-kaca da shi.
Darakatan yada labarai na hedikwatar rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce jirgin ya sauƙa ne a ƙasar ta yammacin Afirka saboda “matsalar na’ura”.
“Rundunar sojin saman Najeriya tana son ta yi bayani kan rahotanni game da yada zangon jirginta ƙirar C-130 a kan hanyarsa ta zuwa ƙasar Portugal ranar 8 ga watan Disamba na shekarar 2025.
Bayan tashin jirgin daga Legas, jami’ai sun lura da wata matsalar na’ura lamarin da ya tilasta saukarsa a Bobo-Dioulasso, Burkina Faso, filin jirgi mafi kusa, kamar yadda ya dace a tsarin kariya da na tuƙin jirgi a duniya,” a cewar Ejodame a wata snaarwar da ya fitar ranar Talata.
Rahotanni dai sun ce hukumomin Burkina Faso sun kama jami’ai 11 kan keta sararin samaniyarta.
Sai dai kuma, Ejodame ya ce dukkan jami’an rundunar sojin saman Najeriya “suna cikin aminci kuma sun samu tarba mai kyau daga hukumomin da suka karɓe su”.
“Ana shirin ci gaba da tafiyar kamar yadda aka tsara ,” a cewar sanarwar.