Matafiya a Indiya sun shiga rudani bayan kamfanin zirga-zirgar jiragen sama mafi girma a ƙasarIndia ya soke tashin ɗaruruwan jirage a yau Juma’a.
Kamfanin da ke da kashi 60 cikin 100 na kasuwar Indiya gaba ɗaya kuma ya ke da jiragen fasinja fiye da 2,000 duk rana, ya sha fama da ƙarancin matuƙa jirgi saboda gaza fara amfani da sabon tsarin aiki na gwamnati.
Dubunnan fasinjoji ne su ke ƙasa jibge a Indiya a daidai lokacin da ake yawan tafiye-tafiye na ƙarshen shekara, kuma a yanzu an soke dukkanin jirage daga Delhi babban birnin ƙasar.
IndiGo ya ce za a koma bakin aiki nan da 10 ga watan Fabarairu, amma ya nemi a sassauta sababbin dokokin da suka bai wa direbobi lokutan hutu da kuma rage ayyukan dare.