Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiTinubu ya tafi Saudiyya domin Umara da yi wa Najeriya addu’a

Tinubu ya tafi Saudiyya domin Umara da yi wa Najeriya addu’a

Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja zuwa birnin Makka na ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umara da kuma yin addu’o’i ga Najeriya.

Tawagar da ta raka shugaban ƙasar ta haɗa da gwamnonin jihohin Kwara, Borno, Kaduna, Sokoto, Jigawa da Yobe, tare da wasu ministocin gwamnatin tarayya.

Tinubu ya tashi ne daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, jim kaɗan bayan ƙaddamar da wasu sabbin kayan aiki da Rundunar Sojin Saman Najeriya ta saya domin gudanar da ayyukanta.

Yayin ziyarar, ana sa ran shugaban ƙasar zai gudanar da ibadar Umara tare da yin addu’o’in zaman lafiya, tsaro da ci gaban Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments