Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 2 ga Disamba, 2026, domin yanke hukunci kan ƙarar neman diyyar Naira biliyan ɗaya da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa El-Rufai ya shigar da ƙarar ne a kan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC, Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta sanya ranar yanke hukuncin, bayan lauyoyin ɓangarorin da ke shari’ar sun gabatar tare da amincewa da takardun hujjojin da suka shigar gaban kotu.