Friday, November 6, 2026
HomeLabarai’Yan sanda sun kama mutane uku bisa zargin satar wayoyin lantarki a...

’Yan sanda sun kama mutane uku bisa zargin satar wayoyin lantarki a Jigawa.

Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama mutane uku bisa zargin lalatawa da satar wayoyin lantarki a ƙananan hukumomin Guri da Dutse na jihar.

Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama mutane uku bisa zargin lalatawa da satar wayoyin lantarki a ƙananan hukumomin Guri da Dutse na jihar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Shiisu Lawan Adam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 24 ga Oktoba, 2026, a Dutse.

A cewar sanarwar, ’yan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 23, mai suna Abdullahi Maina, ɗan asalin ƙaramar hukumar Nguru ta Jihar Yobe, a ranar 21 ga Oktoba da misalin ƙarfe 9:30 na safe. An same shi da babbar wayar lantarki mai ƙarfin wutar lantarki da ya ɓoye a cikin buhu a Guri.

Haka kuma, jami’an ’yan sanda a Dutse sun kama wasu mutane biyu, Ahmed Garba mai shekaru 20 da Abdullahi Garba mai shekaru 25, waɗanda mazauna garin Jigawar Tsada ne. An kama su da misalin ƙarfe 3:00 na dare a harabar Cibiyar Bunƙasa Ƙwarewa ta Manpower Development Institute (MDI), bisa zargin haɗa baki da shiga cibiyar ba bisa ƙa’ida ba da satar wayoyin lantarki masu kariya.

Rundunar ta ce dukkan waɗanda ake zargin suna tsare, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano yadda lamarin ya faru da kuma ko akwai wasu da ke da hannu. Ta ƙara da cewa za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike a sashen binciken manyan laifuka na jihar da ke Dutse.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Tijjani Murtala, ya jaddada aniyar rundunar na kare kadarorin jama’a da kayayyakin more rayuwa. Ya kuma buƙaci al’umma su riƙa kai rahoton duk wani abu da suka gani na shakku ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments