Friday, November 6, 2026
HomeSiyasaBauchi: APC ta musanta kulla yarjejeniya da Bala Mohammed da APM

Bauchi: APC ta musanta kulla yarjejeniya da Bala Mohammed da APM

Jam’iyyar APC reshen Jihar Bauchi ta musanta rahotannin da ke cewa ta ƙulla yarjejeniyar siyasa da Gwamna Bala Mohammed da jam’iyyar APM.

Sakataren yaɗa labaran APC a jihar, Shehu Udubo, ya ce jam’iyyar ba ta da masaniya kan wata yarjejeniya irin wannan, inda ya buƙaci jama’a da su yi taka-tsantsan wajen yaɗa rahotannin.

Udubo ya shawarci Gwamna Bala Mohammed da ya koma APC a hukumance idan da gaske yake son haɗa jihar da gwamnatin tarayya domin samar da ayyukan ci gaba.

Ya bayyana cewa ci gaba da alaƙar gwamnan da APM, ciki har da yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam’iyyar, ya haifar da shakku kan rahotannin yarjejeniyar da ake cewa an ƙulla da APC.

Jam’iyyar APC ta ce haɗin kai da gwamnatin tarayya zai taimaka wajen jawo ayyukan ci gaba, faɗaɗa damar jihar ta amfana da shirye-shiryen gwamnatin tarayya da kuma inganta rayuwar al’ummar Bauchi.

APC ta kuma jaddada goyon bayanta ga manufofin Shugaba Bola Tinubu, tare da kira ga mazauna jihar da su ba da muhimmanci ga shugabanci nagari, zaman lafiya da ci gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments