Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar da kashi na uku na babbar hanyar Abuja–Kaduna–Zariya–Kano, wadda ta haɗa Zariya da Kano, domin inganta zirga-zirga, rage haɗurra da bunƙasa kasuwanci a Arewacin Najeriya.
An gudanar da bikin ƙaddamar da hanyar ne ranar Laraba, inda Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya wakilci shugaban ƙasar.
Hanyar na daga cikin manyan hanyoyin sufuri da ke haɗa Kano da Kaduna da sauran sassan ƙasar, inda dubban matafiya, ’yan kasuwa da masu motocin haya ke amfani da ita a kullum.
Ana sa ran kammala aikin zai inganta yanayin hanya, rage haɗurran da ke faruwa sakamakon lalacewar kwalta, tare da sauƙaƙa jigilar kayan amfanin gona da sauran kayayyaki tsakanin Kano, Kaduna da jihohin da ke makwabtaka da su.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa Tinubu bisa ba da fifiko ga manyan ayyukan more rayuwa. Ya ce ingantattun hanyoyi na da muhimmanci wajen haɗa al’umma, bunƙasa kasuwanci da samar da yanayin da zai taimaka wa tattalin arziki.
Gwamnan ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta ci gaba da gyara da gina hanyoyi masu ɗorewa a Kano, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi. A ƙarshe, gwamnatin Kano ta yi kira ga masu ababen hawa da su kiyaye dokokin hanya, su guji wuce gona da iri wajen gudu da kuma kauce wa wucewar haɗari domin kare rayukan matafiya.