Jiga-jigan jam’iyyar APC da dubban magoya bayanta daga jihohi shida na Arewa ta Tsakiya sun gudanar da wani gagarumin gangami a Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa, domin nuna goyon bayansu ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, a zaɓen 2027.
Taron ya samu halartar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, da gwamnonin jihohin yankin, tare da sauran manyan jami’an gwamnati da shugabannin jam’iyyar.
A jawabansu, shugabannin APC sun bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa sun sa suka yi imanin cewa ya kamata a sake ba shi dama ta wa’adi na biyu.
Sun kuma yi kira ga al’ummar Arewa ta Tsakiya da su haɗa kai wajen tallafa wa Tinubu da Shettima a zaɓen 2027, inda suka jaddada cewa za su ba da duk gudunmawar da ake buƙata domin cimma wannan buri.
A nata jawabin, Oluremi Tinubu ta jaddada muhimmancin shigar mata cikin harkokin siyasa da kuma wayar da kan masu zaɓe game da manufofi da shirye-shiryen gwamnatin tarayya.